1 Thessalonians 4

Rayuwa don a Gamshi Allah

1A ƙarshe, ʼyanʼuwa, mun umarce ku yadda za ku yi rayuwa domin ku gamshi Allah, kamar yadda kuke yi. Yanzu muna roƙonku muna kuma gargaɗe ku a cikin Ubangiji Yesu ku yi haka sau da sau. 2Gama kun san umarnan da muka ba ku ta wurin ikon Ubangiji Yesu.

3Nufin Allah ne a tsarkake ku: cewa ku guje wa fasikanci; 4don kowannenku yǎ koya yadda zai kame kansa a hanyar da take mai tsarki, mai mutunci kuma, 5ba cikin muguwar shaʼawa kamar ta marasa bangaskiya, waɗanda ba su san Allah ba; 6cikin wannan alʼamari kuwa kada wani yǎ yi wa ɗanʼuwansa laifi ko yǎ cuce shi. Ubangiji zai hukunta mutane saboda dukan irin waɗannan zunubai, kamar yadda muka riga muka gaya muku, muka kuma yi muku gargaɗi. 7Gama Allah bai kira mu ga zaman marasa tsarki ba, sai dai ga zaman tsarki. 8Saboda haka, duk wanda ya ƙi wannan umarni ba mutum ne ya ƙi ba sai ko Allah, wanda ya ba ku Ruhunsa Mai Tsarki.

9Yanzu kuwa game da ƙaunar ʼyanʼuwa, ba ma bukata mu rubuta muku, gama ku kanku Allah ya riga ya koya muku ku ƙaunaci juna. 10Gaskiyar kuwa ita ce, kuna ƙaunar dukan ʼyanʼuwa koʼina a Makidoniya. Duk da haka muna ƙara gargaɗe ku, ʼyanʼuwa, ku yi haka sau da sau.

11Ku mai da wannan burinku na yi natsattsiyar rayuwa, kuna mai da hankali ga shaʼanin da yake gabanku, kuna kuma yin aiki da hannuwanku, kamar dai yadda muka gaya muku, 12don rayuwanku ta kullum ta zama da mutunci ga waɗanda suke na waje don kuma kada ku dogara a kan kowa.

Zuwan Ubangiji

13ʼYanʼuwa, ba ma so ku kasance cikin jahilci game da waɗanda suka yi barci, ko kuwa ku yi baƙin ciki kamar sauran mutanen da ba su da bege. 14Mun gaskata cewa Yesu ya mutu ya tashi kuma daga matattu, ta haka muka gaskata cewa Allah zai kawo waɗanda suka yi barci a cikinsa tare da Yesu. 15Bisa ga maganar Ubangiji kansa, muna gaya muku cewa mu da muke raye har yanzu, waɗanda aka bari har dawowar Ubangiji, tabbatacce ba za mu riga waɗanda suka yi barci tashi ba. 16Gama Ubangiji kansa zai sauko daga sama, da umarni mai ƙarfi, da muryar babban malaʼika da kuma busar ƙahon Allah, waɗanda suka mutu kuwa cikin Kiristi za su tashi da farko. 17Bayan haka, mu da muke da rai da aka bari, za a ɗauke mu tare da su a cikin gizagizai don mu sadu da Ubangiji a sararin sama. Ta haka za mu kasance tare da Ubangiji har abada. 18Saboda haka ku ƙarfafa juna da waɗannan kalmomi.

Copyright information for HauSRK